Gangamin gurgunta kasuwanci a Hongkong

Dubun dubatar masu kare dimokradiya sun fara wani gangami domin gurgunta harkokin kasuwanci a Hongkong

Wata Kungiya dake kiran kanta Occupy Central ita ce ta sanar da haka a dai dai lokacin da dalibai dake fafutuka ke ta taho mu gama da jamian 'yan sandan.

Daliban na ci gaba da nuna fushinsu akan hukumomin China kan kin baiwa yankin na Hong Kong cikakken ikon mulkin dimokradiya.

Zanga zangar dai na ci gaba da gudana ne, tun bayan da daliban suka mamaye wani danadali dake wajen hedkwatar gwamnati a ranar Juma'ar da ta gabata.

Sun nemi a janye sabbin kaidojin da gwamnatin China wadda ke iko da yankin Hong Kong ta dauka akan yadda za'a gudanar da zaben shugaban yankin a shekarar 2017.

Masu zanga zangar sun kuma ce ya kamata a sake dawowa da batun tuntubar jama'a akan sauye sauyen da za'a yi wa tsarin mulkin dimokradiyar yankin