Zan so na koma gida Sudan inji Meriam Ibrahim

Meriam da Mijinta
Image caption Meriam da Mijinta

A karon farko matar nan 'yar kasar Sudan da aka yankewa hukuncin kisa bayan da ta yi ridda, ta fito baina jama'a tun bayan da ta isa kasar Amurka a watan Yulin da ya gabata.

Meriam Ibrahim ta karbi lambar yabo daga wata kungiyar addinin Kirista ta conservative dake Washington, saboda jajircewa da ta yi kin sauya ra'ayinta.

A wata hira da ta yi da BBC, ta ce za ta fara da'awar kare hakkokin wadanda ake muzgunawa saboda addinin da suka zaba.

Kamin zuwan ta Amurka, wata kotu a Sudan ta yankewa Meriam hukuncin kisa saboda riddar da ta yi, duk da cewa tana dauke da juna biyu, lamarin da ya jawo suka daga kasashen duniya da dama.