'Yan gudu hijira na wahala a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya, dubban mutanen da suka gudu daga jihohin Yobe da Borno da Adamawa zuwa wasu yankuna sakamakon hare-haren 'yan Boko Haram sun koka a kan mawuyacin halin rayuwar da suke ciki.

A wasu wuwaren dai hukumomi sun bude sansanoni na wadanda tashin hankalin ya raba da muhallansu, inda akan ba su taimako, yayin da akasarinsu ke zaune a gidajen 'yan uwa da abokan arziki.

Koda yake mahukunta da kungiyoyin agaji sun ce suna kokarin taimaka wa 'yan gudun hijira da ke cikin sansani a birnin Gombe, 'yan gudun hijirar da ke zama a gidajen 'yan-uwa da abokan arziki kuwa cewa suke yi basa ma jin duriyar agajin mahukuntan.

Malam Abdullahi Ibrahim, wani dattijo mai 'ya 'ya takwas da mata daya, ya ce hukumomi ba su basu taimako.

Sai dai sakataren hukumar agaji ta jihar Gombe, Dokta Danlami Arabs Rukujei, ya ce a baya sun bada taimako ga 'yan gudun hijirar da ke cikin gari amma yanzu sun fi maida hankali ne ga wadanda ke sansani, kafin su sake komawa ga wadanda ke cikin gari.

A cewar hukumar agajin gaggawa ta jihar Gombe dai akwai 'yan gudun hijira kimanin 15,000 a jihar daga jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa -- kuma galibinsu a cikin gari suke, ba a sansani ba.

A bangare guda kuwa, wata matsalar da 'yan gudun hijirar ke fama da ita musamman kananan yara dake karatu a wuraren da suka baro, ita ce yadda karatunsu ya tsaya kuma basu da tabbas kan makomar karatun nasu ko ci gaba da yinsa.

Abduljamil, wani yaro mai kimanin shekaru 13 da haihuwa wanda tarzoma ta kora daga garin Gwoza na jihar Borno zuwa birnin Gombe, ya ce yanzu ya kwashe shekara biyu ba ya makaranta.

To amma hukumomi sun ce sun bude wani aji na musamman a sansanin 'yan gudun hijirar, inda akan koya wa wasu daga cikin yaran karatu kwatankwacin na firamare.

Karin bayani