Gwamnatin Najeriya ta sake nanata mutuwar Shekau

Abubakar shekau Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Abubakar Shekau jagoran kungiyar Boko Haram

Hukumomi a Najeriya sun ce suna da kwarin gwiwa cewa dakarun kasar sun kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Imam Abubakar Shekau.

A Jiya Juma'a ne dai gwamnatin Amurka ta ce ba ta samu wata shaida da za ta tabbatar mata da ikrarin gwamnatin Najeriya ba, dangane da mutuwar shugaban kungiyar ta Boko Haram ba.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Rodney D. Ford, ya ce yanzu haka suna ma kokarin ne na tabbatar da ko gwamnatin ta Najeriya ta yi wannan ikrarin.

Sai dai Mista Mike Omeri, wanda shi ne shugaban cibiyar ba da bayanai ta kasa, ya ce gaskiya hukumomin sojin Najeriyar suka fada game da mutuwar Shekau.

Ya ce da farko akwai Abubakar shekau wanda aka kashe amma daga bisani wani jagoran kungiyar ya bulo da lakabin Shekau kuma shi ma ba a jima da kashe ba.