Shirin yaki da rashawa ta hanyar amfani da waya a Uganda

Hakkin mallakar hoto EPA

An bulo da wani shirin yaki da rashawa ta hanyar amfani da wayoyin tafi da gidanka a kasar Uganda.

Wani malami dake koyarwa a wata makarantar frimare ta gwamnati dake wajen garin Kampala ya ce matsalar rashawa ta shafi yadda suke gudanar da ayuikansu saboda jinkirin da ake fuskanta wajen samun kudin siyan alli.

Ya ce a wasu lokutan malami ke sayan alli da kudinsa ko ya karbo a matsayin bashi .

Mr Douglas Buule ya ce rashin kudin ya sa daliban makarantar da yawansu ya kai 529 kan rubutu jarabawa sau biyu a fatarar karatu a maimakon a kowani wata .

Malamin ya ce akwai rashin gaskiya a cibiyoyin gwamnati akan yadda ake samar da kudade da kuma yadda ake kashesu inda ya danganta lamarin kan rashawa.

Sai dai yanzu sabon tsarin yaki da rashawa ta hanyar amfani da wayoyin tafi da gidanka da aka kaddamar a wasu yankuna uku a Uganda zasu ba jama'a damar shigar da kara idan aka samu banbanci a kasafin kudin da aka ware wa cibiyoyin lafiya da makarantu da kuma kudin da ya shigo hanunsu.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wayoyin zasu ba mutane damar sanin wurin da makarantun ko cibiyoyin lafiya suke da yawan ma'aikata da ke wurin da kuma yawan kudaden da aka ware masu.

Idan mutane na zargin ana sama da fadi da dukiyar gwamnati misali idan gwamnati ta bayar da kudin shigowa da motar daukar mara lafiya kuma aka samu akasin haka to jama'a zasu iya daukar wayar domin su falasa abin da ya faru.

Zasu iya yin haka ta hanyar aikewa da sako zuwa shafin A4T da kuma shafin sada zumunta na Facebook.

Shugaban shirin Moses Karatunga ya ce idan batu ne da ya kamata a sanar da 'yan sanda zasu yi hakan ko ma'aikatar da aka dora ma alhakin raba kudi.