Ana bikin yaki da fataucin yara a Niger

Hakkin mallakar hoto MARINA MILITARE

Hukumar yaki da fataucin bil-adama ta Jamhuriyar Nijar ta shirya wata muhawara ta musamman domin shawo kan matsalar.

An shirya tattaunawar ce a ranar Lahadi a wajen bikin karrama ranar yaki da fataucin yara da mata.

Wasu dai na danganta matsalar ce da talauci, wanda suka ce ya yi wa jama'a katutu a kasar.

Amma kwararru da jami'an gwamnati sun ce kwadayi da jahilci ne ka haddasa fataucin bil-adama, wanda suka ce doka ta haramta.

Sun dai koka sosai akan batun sanya kananan yara ayyukan da suka fi karfinsu da kuma wasu ayyukan cin zarafinsu.

Sun ce abin da yafi kamari a kasar ta Nijar shi ne irin yadda wasu 'yan kasar ke ketara iyakoki suna tafiya kasashen waje, inda galibi sukan fada cikin mawuyacin hali.

Ko a bara wasu 'yan yankin Kance su 92 sun rasa rayukansu sakamakon kishirwa da yunwa cikin hamada yayin da suke kokarin ketarawa kasar Aljeriya.

Karin bayani