Ebola:Tawagar MDD ta fara aiki a Ghana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar Dunkin Duniya ta ayyana birnin Accra a matsayin Helkwatan Hukumar ta UNMEER

Wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da cutar Ebola za ta fara aiki tare da hukumomin kasar Ghana kan yaki da cutar a yankin yammacin Afrika.

Majalisar Dunkin Duniya dai ta ayyana birnin Accra a matsayin shalkwatar Hukumar da ta kafa kan yaki da Ebola wato UNMEER.

A ranar Litini ne tawagar karkashin jagorancin wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musammam wato Mr. Anthony Banbury ta isa birnin Accra.

Hukumomin kasar Ghana na daukar matakai na hana bullar cutar Ebola a cikin kasarta.