Amurka na sa ido kan yanayi a Hong Kong

Zanga zanga a Hong Kong Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zanga zanga a Hong Kong

Amurka ta ce tana sa ido kut da kut a yanayin da ake ciki a Hong Kong sannan ta kira mahukunta su nuna juriya.

Fadar shugaban Amurka ta White House ta kuma bukaci masu zanga zanga da su bayyana ra'ayoyinsu cikin lumana.

Birtaniya ta ce yalwa da tsaron Hong Kong na tare ne da yanci da kuma walwalarta da suka hada da yancin yin zanga zanga.

Tun farko China ta ce ba za ta lamunci duk wani goyon baya na waje a kan abinda ta kira haramtattun kungiyoyi ba -- tana mai gargadin sauran kasashe da kada su goyi bayan zanga zangar neman kafa demokuradiya a Hong Kong.

Ma'aikatar harkokin waje ta ce tana adawa da duk wata katsalanda a cikin harkokin cikin gida na China.

Tun farko dai dubban masu zanga zanga na ci gaba da zaman dirshan a tsakiyar birnin Hong Kong a matakin nuna goyon baya ga kare c igaban dimokradiyya.

Masu zanga zangar sun fito kwansu da kwarkwata fiye da kwanakin da suka wuce bayan arangama da yan sanda wadanda suka yi amfani hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga zangar a ranar lahadi.

Masu zanga zangar dai na bukatar China ta janye dokokin da suka ba ta damar tantance yan takarar da za su tsaya a zaben da za'a gudanar na gaba.