Niger: Rikici kan zaman majalisar dokoki

A Jamhuriyar Niger dambarwar da ake yi a majalisar dokokin kasar ta sake daukar sabon salo, a wannan karon kuma dangane da zaman majalisar dokokin.

Sabuwar takaddamar ta sake kunno kai ne bayan da kwamitin gudanarwar majalisar ya dauki matakin kiran zaman majalisar a ranar 1 ga watan Oktoba, sai dai daga bisani kuma shugaban majalisar Malam Hama Amadu wanda ke gudun hijira a kasar Faransa shi ma ya sake kiran zaman majalisar a ranar 7 ga watan na Oktoba.

Sai dai bangaren masu rinjayen sun yi watsi da kiran da shugaban majalisar Hama Amadou ya yi, suna masu cewa ba ya bisa ka’ida.

Malam Hama Amadou dai ya jima yana gudun hijira daga kasar, bayan wata takaddama data kunno kai data shafi safarar jarirai wacce ake zargin yana da hannu a ciki.