Rashin bankunan karkara cikas ne ga Nijeriya

Nigeria Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption Karancin bankuna a karkara na kawo cikas ga shirin rage tsabar kudade a Nijeriya

Masana a Nijeriya sun ce akwai bukatar a kara kaimi wajen kokarin tabbatar da rage tsabar kudade a hanun jama'a.

Da dama dai daga kananan hukumomi da ke yankunan karkara a kasar ba su da bankunan da za su yi ma'amala da su, lamarin da kan shafi wannan yunkuri.

Haka kuma kananan bankunan bayar da rance da a wasu lokutan ake kakkafawa, mafi yawa ba sa zuwa ko ina suke durkushewa.

Hakan ya sa wasu da dama ke ganin akwai wuya a iya cimma muradin rage tsabar kudade a Nijeriyar.