Rooney ya bayar da hakuri kan korarsa

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto
Image caption Rooney ya amince cewa ce abinda ya yi bai dace ba

Kyaftin din Manchester United, Wayne Rooney ya baiwa abokanan wasansa hakuri kan korarsa da aka yi a wasansu da West Ham a ranar Asabar.

An kori Rooney a wasan ne bayan da ya yiwa dan wasan West Ham Stewart Downing shigar mugunta.

Har ila yau dan wasan ya ce ba zai daukaka kara akan matakin da alkalin wasan Lee Mason ya dauka akansa ba.

"Matakin ya yi dai dai kuma lallai ina mai bayar da hakuri." In ji Rooney.

Tun da farko shima mai horar da 'yan wasan Manchester United Luis van Gaal, ya ce ya cancanta a kori Rooney saboda abinda ya yi.

Manchester dai ta lashe wasan da ci 2-1 duk da cewa sun buga wasan da mutum 10 a cikin minti 30 na karshe.