'Hankalin 'yan Mogadishu ya kwanta'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Somalia ta shafe fiye da shekaru 20 tana fuskantar tashe-tashen hankula.

Wata cibiya mai nazari kan manufofin kasashen duniya a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, ta ce yanzu hankalin mutanen birnin a kwance yake fiye da yadda yake a shekarar da ta gabata.

Cibiyar wacce ta gudanar da bincike kan mazauna birnin fiye da dubu daya da dari biyar ta ce mutane sun bayyana cewa tashe-tashen hankula sun ragu matuka.

Sai dai har yanzu akwai damuwa kan wasu abubuwa kamar hare-haren mayakan Al-Shabab da rikice-rikice kan hauloli da mallakar filaye da rashin kwarin guiwa kan harkokin shari'a da kuma tsaron kasar.

Kasar Somalia dai ta shafe fiye da shekaru 20 tana fuskantar tashe-tashen hankula.