Julius Malema zai gurfana gaban kotu

Image caption Mr Malema ya yi kaurin suna wajen gangamin yaki da cin hanci da rashawa

A ranar Talata ne za'a fara shari'ar Julius Malema dan siyasa daga bangaren masu adawa a kasar Afirka ta Kudu.

Mr Malema shi ne tsohon jagoran matasan jam'iyar ANC mai mulkin kasar kuma ana tuhumar sa ne da aikata zamba wajen karkata akalar wasu makudan kudade.

To sai dai ya musanta zargi da ake masa wadanda ya bayyana da cewa bita da kullin siyasa ce kawai.

Mr Malema ya yi kaurin suna wajen gangamin yaki da cin hanci da rashawa, inda a watan daya gabata ya jagoranci wani gangami akan shugaban kasar Jacob Zuma da su ke zargi da almubarrazanci da kudaden gwamnati.

To sai dai mambobin jam'iyar sa ta '' Economic Freedom Fighters'' sun ce zasu yi zaman dirshen a kusa da harabar kotun da za a masa shari'ar.