Yau ce ranar kula da lafiyar zuciya

Hakkin mallakar hoto thinkstock

Yau ce ranar kula da lafiyar zuciya ta duniya, da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a kasashen duniya,

Muhimancin wannan rana ita ce kara duba halin da masu fama da cututtukan zuciya ke ciki da kuma zaburar da hukumomi, kan bukatar daukar matakan shawo kan cututtukan na zuciya.

Taken ranar bana shi ne illar amfani da gishiri fiye da kima a abinci.

Masana sun yi gargadin cewa amfani gishiri fiye da kima na cikin abubuwan da ke haddasa cuttutuka irinsu hawan jini.