'Yan takara 7 ne za su fafata a zaben Adamawa

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Har yanzu, tsohon gwamnan jihar na kalubalantar tsigewar da aka yi masa a gaban kotu

Hukumar zabe a Nijeriya ta tantance jam'iyyu bakwai da 'yan takararsu don fafatawa a zaben cike gurbi na jihar Adamawa ranar 11 ga watan Oktoba.

'Yan takarar sun hadar da Sanata Mohammed Umar Jibrilla na jam'iyyar APC da abokin tafiyarsa Martins Babale, sai kuma Ahmadu Umaru Fintiri na jam'iyyar PDP mai mulkin jihar da abokin tafiyarsa Jingi Afraimu Kandamwe.

Sai Aminu Hamman-Joda Furo na jam'iyyar APGA da Aminu Dahiru Abubakar Waziri na Kowa Party da Raymon Mamuno a matsayin mataimakinsa.

Za a gudanar da zaben cike gurbin ne biyo bayan tsige gwamna Murtala Nyako da majalisar dokokin jihar ta yi.

Zaben ka iya zama zakaran gwajin dafi tsakanin manyan jam'iyyun kasar guda biyu, PDP mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta APC.