Na kusa bayyana aniyata —Janar Buhari

Janar Muhammadu Buhari mai ritaya
Image caption Janar Muhammadu Buhari ya yi kira ga magoya bayansa su guji kalaman batanci

Tsohon shugaban Nigeria na mulkin soji, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya ce nan da mako guda zai bayyana aniyarsa ta neman takarar shugabancin kasar.

Janar Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga gamayyar kungiyoyin magoya bayansa a Abuja.

Tsohon shugaban na Nigeria, wanda ya bayyana mulkin jam'iyyar PDP na shekaru 15 a matsayin marar alkibla, ya kuma yi kira ga magoya bayansa su kauce wa batanci da bakaken maganganu a kan abokan takararsa.

A cewar Janar Buhari, "Na yi niyyar bayyana aniyata ranar 8 ga watan Oktoba, kuma ina fatan samun ci gaban goyon baya da sadaukarwa daga gare ku. Sai dai zan so na yi muku nuni cewa in har kuna so goyon bayan ya yi ma'ana sai kun isar da shi ga jam'iyya da dukkan wadanda jam'iyyar ta tsayar".

Ya kuma ce jam'iyyarsu ta APC ce zabin da Nigeria ta dade tana jira, sannan ya kara da cewa sun kuduri aniyar kawo sauyi a yadda abubuwa ke gudana a kasar. Sai dai kuma bai yi cikakken bayani a kan yadda za su kawo sauyin ba.

Karin bayani