Ebola: Marayu na shan tsangwama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rahotanni sun ce kimanin mutane dubu uku ne suka mutu sakamakon cutar Ebola a Afirka ta yamma

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kiyasin cewa kimanin yara dubu biyar ne a Liberiya, Guinea da Saliyo ne suka rasa daya ko duka iyayensu.

Asusun ya ce bai wa yaran kulawa na kara zama mawuyacin abu saboda tsangwamar da suke fuskanta.

Ya ce wasu kananan yaran a wadannan kasashe na samun tallafin abinci daga makwabta, sai dai shi kenan abun da suke iya samu.

Daya daga cikin misalin wadannan yara, shi ne wani yaro dan shekaru hudu da ya rasa iyayensa.

Asusun ya ce an samu mutumin da zai kula da shi, sai dai lamarin bai yi nisa ba saboda al'ummar yankin sun kaurace masa.