Shugaban Hong Kong ya ce ba zai sauka ba

Hakkin mallakar hoto hong kong
Image caption Shugaba CY Leung ya ce zanga-zangar ba zata sa Beijing ta sauya matsaya akan zabe ba

Shugaban Hong Kong C Y Leung ya nuna ba zai sauka daga mukaminsa ba kamar yadda jagororin masu zanga zanga a birnin suka buka ce shi yayi.

A jawabin sa na farko a bainar jama'a tun bayan da masu sha'awar demokradiyya suka fara zanga zanga, Mr. Leung ya bukaci masu zanga zangar da su daina, domin hakan ba zai sauya komai ba.

China ta gargadi kasahen waje da kada su tsoma baki a cikin zanga-zangar bukatar demokradiya a Hong Kong.

Kasar ta kuma dauki tsatstsauran mataki na ta ce rahotannin da kafofin yada labarai na cikin gida suke badawa akan zangazangar.

Masu zanga-zargar wadanda suke kara yawa a birnin Hong Kong, sun tare manyan hanyoyi, sannan suka sa abubuwa suka tsaya cak a wasu sassan birnin.

Masu rajin demokradiyyar suna so gwamnatin China ta bai wa jama'a damar kadakuri'a a zabe na gaskiya, domin su zabi wanda zai zamo shugabansu a 2017.