An tafka gagarumar sata a Cyprus

Hakkin mallakar hoto Rashin Kheyrieh Paintings Exibition NYC
Image caption Zane irin wadannan na da matukar daraja a al'adar Turawa

'Yan sanda a kasar Cyprus sun ce an sace wani zane da wani Bafaranshe Edgar Degas ya yi, wanda darajarsa ta kai yuro miliyan shida kimanin Naira biliyan daya da miliyan 300.

An sace zanen ne mai taken "'Yar rawa na gyara takalminta" a gidan wani mutumin Cyprus ta Girka a birnin Limassol.

'Yan sanda sun ce ba a yi wa zanen inshora ba.

Barayin wadanda 'yan sanda suka yi imanin cewa sun san mai zanen, sun kuma yi awon gaba da agogunan zinare da abubuwan hangen nesa.

'Yan sanda sun kama wani mutumin Cyprus yayin da suke neman karin wasu mutane biyu da ake zargi, dan Rasha da wani dan Afirka ta kudu.