Malala za ta raba kyautar Nobel da Satyarthi

Kaylash Satyarthi da Malala Yousefzai Hakkin mallakar hoto AFP

An bada kyautar lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya ga mutane 2 dake fafutika kan hakkin yara.

Sune Malala Yousefzai ,yariyar nan yarmakaranta ta Pakistan da yan Taliban suka harba saboda gwagwarmayar da take kan ilmin yan mata, da kuma Kailash Satyarthi, wani mai fafutika game da bautar da yara yan mata da kuma kwadagon fansar kai.

Kwamatin Nobel ya ce Malala Yousafzai ta kasance abar misali a wani yanayi mai hadari - yayinda Mr Satyarthi ya dauki halayyar Ghandi wajen yaki da cutar da kananan yara.

Mr Satyarthi ya fadawa BBC cewa kyautar sa girmamawa ce ga al'umar kasar Indiya da kuma duk kananan yara dake aikin bauta.

Firaministan kasar Pakistan Nawaz Sharif, ya bayyana cewa kyautar da Ms Malala ta samu ta sa kowane dan kasar Pakistan yin alfahari a duniya.

Karin bayani