Kananan hukumomi za su samu cikakken iko a Najeriya

Harabar majalisun dokokin na kasa a Najeriya Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Harabar majalisun dokokin na kasa a Najeriya

Majalisar wakilai a Najeriya ta amince da daidaita wa'adin shugabannin kananan hukumomi ya zuwa shekaru hudu kamar yadda sauran zababbun shugabanni ke yi a kasar.

Majalisar ta kuma amince cewar kananan hukumomi su samu cikakken iko, wani al'amari da aka dauki lokaci mai tsawo ana takaddama a kai.

Majalisar ta amince kan haka ne lokacin da ta amince da rahoton kwamitinta mai daidaita matsayarta da ta majalisar dattijai a kan al'amuran gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.

A cikin watan yulin bara ne dai majalisar ta kammala babbar muhawara kan gyaran fuska a wasu sassan kundin tsarin mulkin kasar