Shafin Ello na samun karbuwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu masana sun yi gargadin cewa shafin Ello zai iya fuskantar kalubale da dama.

Shafin sada zumunta na Ello ya ce yana samun bukatar neman shiga dandalin sa daga wajen mutane fiye da dubu talatin da daya a kowace sa'a guda.

Mutumin da ya kirkiri shafin Paul Budnitz ya shaidawa BBC cewa tun da farko an tsara shafin ne domin amfanin ma'abota da ba su wuce casa'in ba.

Ana yi wa shafin lakabi da su na "Mai adawa da Facebook" saboda alwashin da ya yi na kin sanya tallace-tallace ko kuma sayar da bayanan masu amfani da shafin.

Sai dai wasu masana sun yi gargadin cewa shafin na iya fuskantar kalubale da dama.

An dai tsara shafin ne ba tare da sanya abubuwa da dama ba, kuma shafin bai da juriya ga masu amfani da shi kamar sauran shafukan sada da zumunta.

Hakkin mallakar hoto ELLO
Image caption Paul Budnitz yana da shagon sayar da babura ne a jihar Vermont ta Amurka.

Shi dai Paul Budnitz yana da shagon sayar da babura ne a jihar Vermont ta Amurka.

Mr Budnitz ya kara da cewa ya ji kamar ana zuga shi ganin yadda ake kwatanta shafin a matsayin "Mai adawa da Facebook" sai dai ya ce ba haka ya ke ba.

"Ya ce ba ma kallon Facebook a matsayin abokiyar gasar mu, muna kallon shafin ne a matsayin wani dandali na tallace tallace, mu kuma na mu shafin sada zumunta ne".