Hukumomi sun ce sun fatattaki Al Shabaab

Image caption A kwanakin baya ma, jirgin Amurka maras matuki ya kai hari kan ayarin motocin shugaban Al Shabaab a Somaliya

Hukumomi a arewacin yankin Somaliya mai kwarya-kwaryan 'yancin cin gashin kai Puntland, sun ce sun sake kwace wani muhimmin yankin tsauni daga kungiyar Al Shabaab.

Yankin tsauni na Galgala na hannun kungiyar Al Shabaab tsawon shekaru, inda ya kasance babban sansaninsu a arewaci.

Kungiyar Al Shabaab ta ce ana gwabza kazamin fada a yankin amma dai ta ce har yanzu tana iko da iyakokinta.

A kudancin Somaliya kuma, dakarun tarayyar Afirka da sojojin gwamnatin kasar na ci gaba da dannawa birnin Brava mai gabar teku.

Babbar tungar kungiyar Al Shabaab na yankin kudancin Somaliya ne.