An bai wa masu jirage sabon umurni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fiye da jiragen Boeing 1,300 za a bukaci a sauya tsarin na'urorin nuna bayanai ga matuka

An umurci kamfanonin sufurin jiragen sama a Amurka su sauya tsarin wasu na'urori a cikin gaban jiragen Boeing, wadanda matukan jiragen ke amfani da su wajen samun bayanai da sanin alkibla.

Hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Amurka ta ce wasu gwaje-gwaje da akayi, sun nuna cewa sadarwar wayoyin salula da kuma kwamfutoci su na iya sa fuskokin na'urorin cikin jiragen su dauke bayanan da suke nunawa.

Jiragen da matsalar ta shafa, suna da na'urorin nuna bayanai iri daban-daban, kuma an kashe makudan kudade wurin sanya kowanne dayansu.

Kamfanin Honeywell da ke kera nau'rorin ya ce matsalar dauke bayanan, a wurin gwaje-gwaje ne kadai aka sameta, amma ba a taba cin karo da ita ba lokacin da jiragen suke a sama da fasinjoji.

''Matsalar da muka san da faruwarta itace wadda aka samu lokacin gwaji a kasa'' inji kakakin Honeywell Steve Brecken.

''Mun yi aiki tare da kamfanin Boeing a 2012 kuma mun magance dukkan matsalolin na'urorin nuna bayanai da alkibla a cikin jiragen'' Brecken ya ce.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jiragen sama suna da na'urorin nuna bayanai iri daban-daban

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka ta ce ta damu matuka, da yadda hanyoyin sadarwa na wayoyin salula, da na'urorin hasashen yanayi za su iya kawo matsala ga na'urorin da matukan jiragen sama ke ganin bayanai da alkibla.

Hukumar ta ce fiye da jirage 1,300 na Boeing 737 da 777 za su bukaci sauya tsarin na'urorin da matukan ke sanin abinda ke faruwa da kuma yanayin hanya a sama.

''Mun bada wannan umarni ne domin kaucewa yanayin da zai sa matukan jiragen sama su kasa ganin wasu muhimman bayanai a lokutan tashi ko sauka, wanda zai iya sa jirgi ya kwace'' inji hukumar.

Hukumar ta ce ta yi kiyasin aikin sauya tsarin na'urorin zai ci kudi kimanin dala miliyan sha uku da dubu dari takwas.

Hukumar ta ce kamfanonin sufurin jiragen sama na Virgin Australia, da Air France, da Ryanair da Honeywell suna daga cikin wadanda suka soki sabon umurnin, saboda suna ganin karfin sigina ta sadarwar wayoyin salula da na intanet bai kai ya hana na'urorin nuna bayanai a jirage aiki ba.