Yunwa ta hallaka mutane 100 a Congo

Hakkin mallakar hoto non credit
Image caption Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo na fama da rikice-rikicen 'yan tawaye tsawon shekaru

Kungiyar kare hakkin dan'adam ta Human Rights Watch ta ce mutane fiye da 100 ne suka mutu sakamakon yunwa da cutuka a wani sansanin soja da ke Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

Kungiyar ta ce an kai tsoffin mayaka, tare da mata da 'ya'yansu sansanin da ke kebabben yankin arewacin Kongo bayan sun mika wuya a yankin gabashin kasar da yaki ya daidaita.

Rahotanni sun ce an bai wa mutanen abincin da bai kai ya kawo ba, sannan kuma ba sa samun cikakkiyar kula da lafiya, yayin da wasu suka dinga rayuwa a kan amfanin gonar da aka sato daga manoma.

Gwamnatin Kongo dai ta ce tana gudanar da bincike a kan al'amarin.