Cutar Ebola ta bulla a Amurka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An kwantar da mutumin da ya kamu da Ebola a asibiti a Dallas na Texas

Cibiyar kawar da cututtuka da kare lafiyar jama'a ta Amurka ta tabbatar da cewa an samu wani Ba Amurke a Texas da ya kamu da cutar Ebola.

Daraktan cibiyar, Tom Frieden ya ce cutar ta shiga jikin mutumin ne a Liberia, amma bai nuna alamunta ba sai da ya koma Amurka.

A ranar 19 ga watan satumba mutumin ya koma Amurka wajen iyalinsa, amma a lokacin babu wata alama da cutar ta nuna a jikinsa sai a ranar 24.

Wannan ne karo na farko da da aka samu Ba- Amurke dauke da cutar Ebola a cikin kasar, amma a baya wasu 'yan kasar biyu sun kamu da cutar a yammacin Afrika.

Jami'an Amurka sun ce suna da yakinin za su hana cutar yaduwa a kasar.

A jihar Texas din, ana kokarin cimma duk mutanen da sukayi mu'amala da mutumin da kuma wasu a ake tunanin suna cikin hadarin kamuwa da cutar.