Jonathan: Za mu yi nasara kan 'yan ta'adda

Image caption Shugaba Jonathan ya an samu cigaba a shekaru 54 da samun 'yan cin kai

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa don ganin masu ayyukan ta'addanci a kasar ba su yi nasara ba.

A jawabinsa ga jama'ar kasar a kan cikar Nigeria shekaru 54 da samun 'yancin kai, shugaba Jonathan ya ce gwamnati ta dukufa wajen tabbatar da tsaron dukkan jama'ar kasar ba tare da la'akari da inda suka fito ko addininsu ko kuma akidarsu ta siyasa ba.

Ya ce duk da kalubalen tsaro da kasar ke fama da shi, an samu ci gaba ta fannin bunkasar tattalin arziki, da aikin gona da kuma rage matsalar yunwa a kasar.

Shugaban ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen aiwatar da rahoton babban taron kasa da aka kammala kwanan baya.

A 'yan shekarun nan dai, Nigeria ta yi ta fama da matsaloli na tsaro da suka hada da hare-haren kungiyar Boko Haram.