Iraqi: Al Abadi a tunkari IS daga tushe

Hakkin mallakar hoto .

Pira Ministan Iraqi Haider al Abadi ya shaidawa BBC cewa yana mai adawa da shigar kasashen larabawa cikin hare-haren da ake kaiwa ta sama kan mayakan IS a cikin Iraqin.

Sai dai ya kara da cewa abin lallai ya kai makura cewa har kasashen larabawa sun kai hari kan sansanonin mayakan a makwabciyar kasar Syria.

Yace ba tare da yin hakan ba, ba zai iya samun galaba kan kungiyar ISIS a Iraqi ba. Muddin ana son samun galaba kan mayakan ISIS, to fa dole sai an lalata sansanoninsu a Syria.

To amma shi a matsayina na Pira ministan Iraqi ba zai yi kasancewa cikin wadanda zasu kaddamar da hari kan Syria ba saboda makwabciyar kasarsa ce.