An tuhumi masu kirkiro Xbox One na boge

Hakkin mallakar hoto Microsoft
Image caption Darajar kudin mallakar fasahar da aka sace ta kai kimanin dala miliyan100 zuwa dala miliyan 200.

An tuhumi wasu mutane hudu a Amurka da kuma wani mutum guda a Australia bisa zargin su da hannu wajen satar bayanan wasannin bidiyo a lokacin da ba a kaiga fitar da shi.

Masu shigar da kara sun yi zargin cewa mutanen sun yi kokarin amfani da bayanai da suka sa ce wajen kirkiro na'urar wasannin bidiyo na X Box One na boge.

An bayyana cewa an sayar da kowane daya daga cikin na'urar bogen a eBay kan kudi dala dubu biyar gabanin bukin kaddamar da shi.

Image caption Ma'aikatar shari'ar ta Amurka ta ce biyu daga cikin wadanda ake zargi sun amsa laifin da ake tuhumar su akai.

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ce darajar mallakar fasahar da kuma bayanan da aka sace sun kai kimanin dala miliyan 100 zuwa dala miliyan 200.

Ma'aikatar shari'ar ta kara da cewa, biyu daga cikin mutanen da ake zargi Sanadodeh Nesheiwat daga New Jersey da David Pokora daga jihar Ontario na Canada sun amsa laifin da ake tuhumar su akai.

Wadanda ake zargi dai ka iya fuskantar daurin shekaru biyar a gidan fursuna idan aka yanke musu hukunci a watan Janairu.

Kamfanin Microsoft bai fito da Xbox One ba har sai a watan Mayu shekarar 2013, kuma ba'a fara sayar da na'urar ba sai a watan Nuwamba.