Sojoji 97 sun gurfana gaban kotun soja

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A baya ma, sai da wasu matan sojoji a Nigeria suka yi zanga-zanga a kofar bariki don hana tura mazajensu filin daga

Wata kotun soja a Nigeria na tuhumar wasu sojoji 97 a kan zarge-zargen da suka hadar da nuna ragwantaka da bijirewa zuwa fafatawa a rikicin 'yan tada-kayar-baya a arewa maso gabashin kasar.

Shari'ar sojojin ta Alhamis din nan na zuwa ne, bayan yanke wa wasu sojoji 12 hukuncin kisa ta hanyar bindigewa saboda yin bore da yunkurin kashe babban kwamandansu.

Sau da dama, dakarun Nigeria suna korafin cewa 'yan Boko Haram sun fi su karfin makamai, kuma ba a biyansu cikakkun hakkokinsu, ana kuma yin biris da su a fagen daga ba tare da isassun albarusai da abinci ba.

Rahotanni sun ce miliyoyin daloli ne suka bace a kasafin kudin da ake yi na yaki da ayyukan 'yan tada-kayar-bayan tsawon shekaru biyar, sakamakon cin hancin da ya zama alakakai a Nigeria.

Sai dai a wani jawabinsa, shugaban kasar Goodluck Jonathan ya jinjina wa sojojin kasar saboda "kishin kasa" da suke nunawa wanda ya ce ya mayar da hannun agogo baya ga kungiyar Boko Haram.