Za a bude taro kan Ebola a Burtaniya

Hakkin mallakar hoto spl
Image caption Burtaniya ta fi kowacce kasa taimakawa Saliyo yaki da Ebola

A yau ne jami'an gwamnatin Burtaniya da na Saliyo za su fara wani taro a London don tattauna yadda za a shawo kan yaduwar cutar Ebola a yammacin Afrika.

Burtaniya dai ta yi alkawarin taimakawa Saliyo da kayayyakin yaki da cutar a wani asibitin mai gadaje 700.

Daya daga cikin manufofin taron na yau shi ne a janyo hankalin sauran kasashen duniya masu arziki su taimaka wajen yaki da cutar a yankin yammacin Afrika.

A wani labarin kuma, hukumomi a Amurka sun ce sunan Ba Amurken da ya kamau da cutar Ebola a Texas Thomas Eric Duncan.

Wasu iyaye a Amurkan sun fara hana 'ya'yan zuwa makaranta saboda ance Thomas Eric Duncan ya yi mu'amala da wasu dalibai.