Kotu ta garkame wani dan Nigeria a Amurka

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Lawrence ya shafe tsawon shekaru goma yana kokarin kauce wa iza keyarsa zuwa Amurka, amma bai yi nasara ba

Wata kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 25 ga wani shugaban gungun masu fataucin hodar iblis mafi tsada, Koyode Lawrence da ke amfani da babban filin jirgin saman Houston a Amurka wajen safararsa.

An yanke wa dan Nigeria hukunci ne ranar Talata a wata kotun tarayya ta Houston bayan tun da farko ya amsa laifin hada baki don shigar da kayan maye Amurka.

An danganta shari'ar da wasu mutane biyu wadanda ke yi wa Lawrence aiki da aka kama a watan Fabrairun 2001 a filin jirgin saman Houston, Hukumomi sun ce mutanen biyu sun hadiyi kunshin hodar iblis da suka yi fasa kwaurinta daga Nigeria.

Masu shigar da kara sun ce Lawrence mai shekaru 45 galibi yana amfani da daliban kwaleji ne masu shaidar zama 'yan kasashe biyu, Amurka da Nigeria don yi masa fasa kwauri.