Marasa lafiya na sanin ciwonsu a intanet

Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption Akwai manhajojin wayar salula da ke taimakawa masu ciwon suga da hawan jini sanin halin lafiyarsu

Wani bincike ya nuna cewa ana samun karuwar marasa lafiya a Burtaniya da ke zuwa wurin likitocinsu da bayanan irin maganin da suke bukata, bisa bayanan da suma suka samu daga manhajojin wayoyin salula kan sha'anin kiwon lafiya.

Kashi uku na likitocin da aka gudanar da binciken a kansu su ce marasa lafiya suna zuwa musu da shawarorin yadda suke so a duba lafiyarsu.

Amma kashi biyar daga cikin dari na likitocin ne su ka ce shawarorin suna taimakawa.

Manyan kanfanonin kera wayoyin salula da suka hada da Apple da Samsung suna kashe makudan kudade akan samarda fasahohi da mutane zasu iya duba lafiyarsau da su.

Kamfanin binciken sha'anin kiwon lafiya na Cello Health Insight ne ya gudanar da binciken akan likitoci 330.

Darakta a kamfanin Dan Brilot ya ce ''an zo wani lokaci da bayanan da likitoci ke samu daga marasa lafiya ya karu sosai saboda cigaban fasaha''.

''Yadda mutane suke neman bayanai yanzu ya karu, kuma akwai manhajojin wayoyin salula masu bayani akan kiwon lafiya da suke taimakawa mutane''.

Suma likitoci suna amfani da kayayyakin fasahan wajen gudanar da bincike.

Da yawa daga cikin likitocin suna amfani da intanet wajen sanar da juna sababbin bayanai da suke samu daga intanet.

Koda yake wasu na ganin akwai matsala yadda mutane ke duba lafiyarsu da kansu, akasarin likitocin da aka gudanar da binciken akansu sun bada shawarar jama'a su rika yin amfani da kayyaykin fasaha wajen sanin yadda lafiyarsu ta ke.

Fiye da rabin likitocin sun ce manhajojin da aka yi na duba lafiyar don tabbatar da ba a samun kuskure wajen bada magungunan cututtuka suna da alfanu.

Ire-iren manhajojin dai suna iya taimakawa masu fama da ciwon suga da hawan jini sanin yadda lafiyarsu ta ke.