Yau take Sallar layya

A yau musulmin duniya suka fara shgulgulan bikin babbar salla ta layya.

Layya aiki ne na ibada wanda ya samo asali daga Annabi Ibrahim Alaihissalam,wanda kuma malamai ke cewa na koyar da darussa na rayuwa da dama.

Daga cikin fa'dodin layya da malamai kan fadakar akai akwai nuna biyayya ga Allah

A ranar alhamis din da ta gabata ne alhazai daga suka isa Minna, kuma da safiyar juma'a suka dunguma zuwa dutsen Arafat.

Dubun dubatar mahajjata ne suka fita zuwa dutsen na arafat, a lokaci guda kuma motocin safa-safa da aka tanada na ci gaba da jigilar mutane.