Google ya goge dubban hotunan tsaraici

Goole Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Google na fuskantar barazanar kara a kotu

Kamfanin Google ya goge dubban hotunan dake nuna tsaraicin wasu fitattun mutane da aka sato aka wallafa a shafin intanet.

Google ya ce ya share hotunan ne bayan da aka bukaci ya yi hakan, ya kuma rufe shafukan wasu daruruwan mutane.

Wannan lamari ya auku ne bayan da lauyan dandalin shirya fina-finai na Hollywood, Marty Singer ya yi barazanar shigar da kamfanin kara saboda bayyana sirrin mutane.

Wasikar da lauyan ya aikawa kamfanin ta zargi kamfanin na Goole da rashin daukan wani mataki na share hotunan, kana ya ci gaba da yada su.

Ko da yake wasikar bata ambaci takamaiman wadanda take wakilta ba, amma ta nuna cewa matakin yana kare wasu shahararrun 'yan wasa ne na Hollywood.

Akwai fitattun 'yan wasan kwaikwayo irinsu Cara Delevingne da Jennifer Lawrence da aka sato hotunansu aka wallafa a intanet a 'yan kwanakin nan.

An dai buga wasikar a jaridar New York Post wacce aka aiketa ga babban jami'in dake kula da ma'aikatan kamfanin na Google.

"Mu lauyoyin 'yan wasan kwaikwayo mata da dama ne, za kuma su nemi bi musu kadinsu saboda sakacin da Google ya yi na karfafa irin wannan mummunar halayya." Wasikar ta ambata.