Musulmi miliyan biyu na tsayuwar Arafat

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsayuwar Arfat muhimmin bangare ce a cikin rukunnan aikin hajji a Musulunci

Musulmi akalla miliyan biyu ne da suka je kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin bana ke yin tsayuwar Arafat a Juma'ar nan.

A jiya ne alhazan suka isa Minna, kuma da safiyar juma'ar nan ne suka dunguma zuwa dutsen Arafat.

Dubun dubatar mahajjata ne suka fita zuwa dutsen na arafat, a lokaci guda kuma motocin safa-safa da aka tanada na ci gaba da jigilar mutane.

Bayanai sun ce mahukuntan Saudiyya sun kara daukar matakai don tabbatar da ganin aikin hajjin ya gudana cikin nasara da kuma kauce wa matsalolin da aka fuskanta a baya.

Daga cikin tsare-tsare da aikace-aikace da dama da aka yi har da kara gina gadoji, don saukakawa masu aikin hajjin.