An yi Allawadai da kisan Henning

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Allan Henning

Birataniya ta bayyana kisan da 'yan kungiyar masu jihadi suka yi wa Allan Henning da cewa abin kyama ne, kuma alama ce ta rashin hankali.

Firayim Minista David Cameron ya ce Birtaniya za yi bakin kokarinta wajen gano makasan.

A jiya ne dai Kungiyar masu jihadin ta fitar da wani hoton bidiyo, inda ta nuna yadda suka halaka Allan Henning.

Wanda ya kashe shin yana da karen harshen Ingilishin Birtaniya iri daya da na wanda ya halaka wasu da suka gabata.

Kungiyar ta sake nuna wani Ba'amurke a cikin hoton Bidiyon, mai suna Peter Kassig, wani mai aikin agaji, wanda ta yi barazanar cewa za ta halaka shi a nan gaba.

Tuni dai wasu shugabannin musulmi a Birtaniya suka yi Allah-wadai da kisan Henning.

Karin bayani