Maiduguri: Babu zirga-zirga ranar Sallah

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An hana zirga-zirgar motoci da babura a Maiduguri daga yammacin Juma'an nan

A Najeriya, rundunar sojin kasar ta hana zirga-zirgar ababen hawa a Maiduguri babban birnin Jihar Borno daga karfe biyar na yamman yau Juma'a har zuwa ranar litinin.

Rundunar ta dauki matakin ne sakamakon bayanan da ta samu cewa 'yan 'yan kungiyar Boko Haram za su kaddamar da hare-haren bom a Maiduguri da wasu garuruwa lokacin bukukuwan babbar sallah.

Bayanai sun nuna cewa 'ya'yan kungiyar sun kammala shirye-shiryen yin amfani da motoci, da babura masu taya uku da sauran ababen hawa wajen kaddamar da hare-haren.

Rundunar Sojin ta ce wuraren da 'ya'yan kungiyar suke hako, sun hada da masallatan idi, da kasuwanni da kuma sauran wuraren da jama'a ke taruwa.

Kazalika rundunar sojin ta bukaci jama'ar garin Maiduguri da su gudanar da sallar idi a masallatan da ke kusa da gidajensu domin tsaron rayukansu.