Ana zaman makoki a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou ya ce NIjar ba za ta taba ja da baya ba ga ta'addanci

Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwana uku daga yau bayan kashe sojojinta tara a Mali.

Hukumomin kasar da suka lashi takobin cigaba da shiga aikin yaki da ta'addanci a Mali sun ce daga ranar Lahadi zaman zai fara.

A ranar Juma'a ne wasu 'yanbindiga suka yi wa tawagar sojin kasar da ta je Mali aikin zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya kwantan bauna.

Harin shi ne mafi muni da aka kai wa sojin tabbatar da zaman lafiyar na Majalisar.

Dakarun Majalisar dinkin duniya na kokarin dawo da kwanciyar hanakali a arewacin Mali , yankin da ya fada hannun 'yan tawayen Abzinawa da kuam masu kishin Islama.

Karin bayani