Chelsea ta mamayi Arsenal da ci 2-0

Chelsea Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea na haskawa a asamn teburin Premier da maki 19

Chelsea na ci gaba da mallake saman teburin gasar Premier bayan da ta lallasa Arsenal da ci 2-0.

Eden Hazard ne ya fara zira kwallo a bugun fenarti kamin a je hutun rabin lokaci sannan Diego Costa ya kara ta biyun.

A watan Maris din da ya gabata Chelsea ta doke Arsenal da ci 6-0, lamarin da ya dagula lissafin wasan Arsenal na 1000 a karkahsin kulawar Arsene Wenger.

Wannan nasara da Chelsea ta samu ya ba ta damar samun tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City da ke biye da ita a teburin gasar da maki 19.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi a gasar ta Premier

Man Utd 2-1 Everton ; Chelsea 2-0 Arsenal; Tottenham1-0 Southampton ; West Ham2-0 QPR.