An gano wasu kutse a bankunan Amurka

Hacking Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kwashi bayanan akalla mutane miliyan 83 a bankin JP Morgan

Rahotanni daga Amurka na cewa masu kutsen da suka kwashi bayanai a bankin JP Moragn sun shiga kwamfutocin wasu bakuna tara.

Sai dai ba a ambaci sunan bankunan ba baya ga na JP Morgan da aka sanar a farko.

A ranar alhamis din da ta gabata bankin na JP Morgan ya sanar da cewa masu kuste sun shiga cikin kwamfutocin bankin inda suka kwashi bayanan mutane miliyan 83 da na wasu 'yan kasuwa.

Hakan ya baiwa masu kutsen samun sunayensu da adreshi da lambar waya da kuma adreshin email wasu kwastomomin bankin.

Wannan lamari na daya daga satan bayanai mafi girma da aka taba yi a tarihi.

Ya kuma faru ne a dai dai lokacin da kwastomomi ke dari - dari da yanayin kasuwa.

Da farko bankin na JP Morgan ya bayyana cewa asusun wadanda abin ya shafa bai fi na mutane miliyan daya ba.

Jaridar New York Times ta ruwaito cewar rashin sanin dalilan satar bayanan ya fara damun masu tsare-tsare da jami'an tsaron Amurka.