An gano wani makeken kabari a Mexico

Mexico Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana kyautata zaton akwai hanun gungun masu safarar miyagun kwayoyi a kisan

A kasar Mexcio an gano wani makeken kabari a wajen garin Iguala, inda wasu dalibai 43 suka bata sama da mako guda.

Batan daliban ya biyo bayan wata arangama da 'yan sanda suka yi yayin da ayarin daliban ke kan hanyarsa ta halartar wata zanga zanga.

Rahotanni na cewa akwai yuwuwa da hanun gungun masu safarar miyagun kwayoyi a kisan.

Yanzu masu bincike na kokarin gano ko gawarwakin da aka samu a kabarin na daliban da suka bata ne yayin da ake binciken wasu 'yan sanda 22 da ake zargin na da hanu a kisan.