Ana bukukuwan babbar Sallah a Nijar

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Ana can ana bukukuwan Sallah babba a Nijar

A Jamhuriyar Nijar ranar Lahadi ne ake gudanar da shagulgulan babbar sallah a ko'ina cikin fadin kasar.

Majalisar koli ta addinin musulunci ta kasar ce ta yi shelar a yi sallar a ranar Lahadi.

A hudubar da ya yi, babban limamin Yamai ya bukaci 'yan siyasa da su rika yafe wa juna.

Ya kuma yi kira ga 'yan kasar dasu ci gaba da hada kawunansu domin ci gaban kasarsu.