'Ya kamata Blatter ya sauka'

FIFA Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Sepp Blatter ya ce zai sake tsayawa takarar shugabancin hukumar FIFA

Wani mamba a kwamitin gudanarwa na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ya ce idan har ana so a farfado da martabar hukumar ya kamata shugabanta Sepp Blatter ya sauka daga mukaminsa.

A wata hira da ya yi da BBC, Michael Hershman, ya ce saukar Blatter daga mukaminsa zai taimakawa fagen wasanni, wanda hakan zai bude kofar samun sabbin jini.

"Hukumar na bukatar sauyin shugabanci, a duk lokacin da aka ce an samu zarge zarge, ya kamata a samu sauyin shugabanci." In ji Hershman.

Dan shekaru 78, Blatter ya fara shugabantar hukumar ne tun daga shekarar 1998.

A watan da ya gabata ne kuma ya ayyana cewar zai sake tsayawa takarar shugabancin hukumar, duk da cewa ya yi alkawarin cewa wannan wa'adin na hudu da yake ciki shine ne karshe da zai yi.