Za a hau teburin tattaunawa a Hong Kong

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu daga cikin dalibai masu zanga-zangar

Shugabannin dalibai da gwamnatin Hong Kong, sun amince su hau teburin tattaunawa domin lalubo hanyar kawo karshen zanga-zangar da masu rajin kare dumokradiya ke yi.

Wannan bore dai ya janyo rufe wasu manyan titunan birnin na Hong Kong, duk da cewa yawan masu zanga-zangar ya ragu.

Yanzu haka dai hukumomi a Beijing sun ce suna nan akan bakansu, na cewa su za su zabi wadanda za su tsaya zabe a shekarar 2017, lamarin da ya janyo boren.

A ranar Litinin daliban suka bude wasu hanyoyin isa hedkwatar gwamnati, wanda hakan ya bai wa ma'aikata damar komawa bakin aiki.