Makamai: An sake kama kudin Nigeria

Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Makwanni uku da suka gabata an kama wasu 'yan Nijeriya za su je sayen makamai a Afrika ta Kudu

Rahotanni daga Afrika ta Kudu na cewa hukumomin kasar sun sake kama dala miliyan 5.7 ta wata harkar sayen makamai ta bayan gida tsakanin wani kamfanin Afrikta ta Kudun da wani na Najeriya.

Kamfanin Cerberus Risk Solutions wanda ke birnin Cape Town mai sayar da makamai da kuma wani na Nijeriya mai suna Societe D'Equipments Internationaux da ke Abuja ake zargi a wannan lamari.

An gano kudin ne a lokacin da kamfanin na Afrika ta Kudu wanda rijistarsa ta sayar da makamai ta kare ya yi yunkurin mayar wa da kamfanin Nijeriyar kudinsa saboda bai cancanta ya yi hada hadar ba.

Wannan lamari ya bayyana ne kasa da makwanni uku bayan da Afrika ta Kudun ta karbe dala miliyan 9.3 a hannun wasu 'yan Nijeriyar biyu da dan Isra'ila da suka shiga kasar domin sayen makamai ba ta ka'ida ba, da jirgin saman shugaban kungiyar kiristoci na Najeriyar Ayo Oritsejafor.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana da masaniya game da cinikin na dala 9.3 wanda har yanzu ake ta cece-kuce a kansa.