Samsung ya yi hasashen rasa riba 60%

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wayoyi masu araha da suke da tsari irin na Samsung Galaxy din ne suke kashe mata kasuwa

Kamfanin Samsung ya yi hasashen raguwar ribar da yake samu da kashi 60 cikin dari a watanni uku-uku na shekara saboda karancin cinikin wayarsa ta Galaxy.

Kamfanin na Samsung wanda shi ne na daya wajen yin wayoyin salula da talabijin ya ce yana sa ran samun dala biliyan 3.8 na watanni uku zuwa Satumba.

A cikin wannan watan ne za a fitar da bayanan cinikin kamfanin.

Samsung na fafutukar cigaba da zama a gaban abokan gogayyarsa irin su kamfanin Apple da Xiaomi da Lenovo na China.

Wayar Galaxy ta komai-da-ruwanka ta Samsung din ba ta samun kasuwa sosai saboda wasu irinta masu sauki.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wadanda su ma suna da babbar fuska da kuma abubuwa da dama a cikinsu.

Kamfanin na Samsung na Korea ta Kudu, ya ce an samu karuwar fitar da yawan kayayyakinsa zuwa kasuwa saboda gogayya.

To amma kuma ribar da yake samu ta ragu saboda farashi ya yi kasa.

Kamfanin yana kuma fuskantar matsi a bangarensa na kayan laturoni da ke yin talabijin dasauran kayayyaki.

Hakan ya kasance ne sakamakon hawa da tashin darajar kudade da suka sa kayan Japan sauki.