Za a kafa rundunar yaki da Boko Haram

Abubakar Shekau, jagoran kungiyar Boko Haram Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Abubakar Shekau, jagoran kungiyar Boko Haram

A Jamhuriyar Nijar, shugabannin kasashen kungiyar Tafkin Chadi CBLT ko LCBC sun amince su kafa wata rundunar hadin gwiwa a yunkurin yaki da kungiyar Boko Haram.

Hakan na kunshe a karshen taron yini guda da suka kammala ranar Talata, a birnin Yamai, domin nazari kan matsalolin tsaron da ake fuskanta a yankin na tafkin Chadi.

A karkashin tsarin, kowace kasa zata tura sojojinta kan iyakokinta da tafkin na Chadi.

A wata hira da BBC, ministan harkokin wajen Niger , Malam Bazoum Muhammed ya ce a yanzu kasar Kamaru ta amince ta bada cikakken hadin kai, bayan zargin da aka rika ma ta a baya cewa, tana jan kafa a wajen daukar matakan yaki da kungiyar ta Boko Haram.