Abuja: Harkoki ba su kankama ba

Image caption Babu cunkoson ababen hawa a wuraren da aka saba samu

Har yanzu harkokin yau da kullum ba su kankama ba a Abuja, babban birnin Najeriya, sakamakon hutun babbar Sallah na kwanaki biyu da gwamnati ta bai wa ma'aikata a kasar.

A yau Talata hutun zai kare, yayin da ma'aikata a fadin kasar za su koma bakin aiki gobe Laraba.

Sakamakon hutun dai, harkokin cinikayya da zirga-zirgar ababen hawa a Abuja sun ragu, yayin da wuraren da aka saba samun cunkoson ababen hawa da mutane suka zamo sakayau.

A ranar Asabar aka gudanar da Idin babbar Sallah a Najeriya, kuma tun daga ranar kawo yanzu, ana ci gaba da shagulgulan Sallar a sassan kasar daban-daban.