MURIC ta nemi a binciki kudaden da aka kama

Kanar Sambo Dasuki Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Kanar Sambo Dasuki

Kungiyar kare hakkokin Musulmi ta MURIC a Najeriya , ta nemi majalisar dinkin duniya ta gudanar da bincike akan kudaden da hukumomin tsaro na Africa ta Kudu suka kama daga Najeriya.

Kungiyar tace matakin safara da haramtattun kudade, babu abinda ya ke nunawa illa wata rufa- rufa da ake yiwa 'yan Nigeriar

Sai dai gwamnatin Nigeria ta ce kudin da Afirka ta Kudu ta kwace, wanda ta nemi sayen makamai da shi, kudin halal ne kuma cinikin halal ne.

A wata sanarwa da ya fitar, ofishin mai ba da shawarar, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, ya ce kudin da ake magana ba haramtaccen ciniki ake je yi da su ba.